Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu gaskiya cikin rahoton kungiyar Transparency kan batun cin hanci - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi watsi da rahoton baya-bayan nan na kungiyar Transparency International, wanda ya bayyana cewa matsalar cin hanci da Rasahawa a Najeriya kara tabarbarewa ta ke a kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS
Talla

Cikin sanawar da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce babu gaskiya ko kadan cikin rahoton na kungiyar Transparency, da ya nuna Najeriya a matsayin kasa ta 148 daga cikin 180 a jerin wadanda suka jajirce wajen yakar cin hanci da rashawa.

Sanawar ta shawarci Transparency International da ta rika kafa ginshikan rahotannin da take fitar wa bisa dalilai na bayanan gaskiya da kowa ke gani a fili bisa, a maimakon kago rahotanni na son kai.

Malam Garba Shehu, ya ce bayyane yake yadda gwamnatin Najeriya karkashin Muhammadu Buhari, ta toshe kafafen da kudaden kasar ke zurarewa ta hanyar kafa asusun ajiyar kudaden gwamnati na bai daya wato TSA.

Kakakin shugaban Najeriyar ya kara da cewa, alkalumman da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta fitar sun nuna cewa cikin shekaru biyu ta samu nasarar kwato kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 738.9, bayan kama mulkin Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.