Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari na halartar bikin samun 'yancin Ghana

Yau ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kama hanyar tafiyarsa zuwa birnin Accra na Ghana don halartar bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kasar daga turawan mulikin mallaka da za a gudanar a dandalin Independence Square a gobe Talata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFIHausa/Kabiru Yusuf
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina ya ce , Buhari ne kadai shugaban da aka gayyata daga wata kasa don kasance babban bako na musamman a bikin mai cike da tarihi.

Kazalika shugaba Buhari ne kadai aka zaba a matsayin bakon da zai gabatar da jawabi bayan na shugaban kasar Nana Akufo-Addo kamar yadda Adesina ya bayyana.

Adesina ya kara da cewa, shugaba Buhari zai yi amfani da wannan ziyara wajen karfafa dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu.

Ana saran dawowar Buhari gida tare da mukarrabansa da su ka hada da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno a gobe Talata da zaran an kammala bikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.