Isa ga babban shafi
Najeriya-Ghana

Gobe Buhari zai kai ziyarar wuni guda a kasar Ghana

Gobe Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Ghana, don tattaunawa da takwaranshi John Dramani Mahama, kan harkokin tsaro a yankin yammacin Africa.

Shugaban Najeriya,  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari twitter
Talla

Sanarwar da fadar shugaban ta fitar, tace yayin ziyarar ta wuni daya, shugaba Buhari daya ciki kwanaki 100 da karbar madafun ikon kasar, zai kuma tattauna kan lamuran da suka shafi kasuwanci tsakanin kasashen 2.
Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, manyan jami’an ma’aikatun harkokin waje, tsaro, shari’a da na ciniki ne zasu yiwa shugaba Buhari rakiya yayin ziyarar.
Dama a kwanakin baya ya ziyarci wasu kasashen dake makwabta na Najeriya, da suka hada da Kamaru, Chadi, Nijar da Benin, a wani yunkuri na neman hadin kai wajen murkushe kungiyar Boko Haram, da tayi sanadiyyar rasa ran fiye da mutane dubu 15, wasu fiye da miliyon 2 suka tsere daga gidajensu, cikin shekaru 6 da suka gabata.
Kasshen sun yi alkawarin bayar da gudunmawar sojoji da ‘yan Sandan da zasu tunkarin mayakan na Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.