Isa ga babban shafi

JMPP ta sha alwashin zagaye Najeriya da katanga

Shugaban Jam’iyyar JMPP da ke Najeriya Olusegun Ijagbemi, ya sha alwashin sauya suna da kuma kudin kasar, hadi da zagaye kasar da Katanga, idan suka yi nasarar lashen zaben shugaban kasa a 2019.

Mukaddashin shugaban sabuwar jami'yyar JMPP a Najeriya dakta Olusegun Ijagbemi.
Mukaddashin shugaban sabuwar jami'yyar JMPP a Najeriya dakta Olusegun Ijagbemi. Concise News
Talla

Mista Ijagbemi wanda ya ce, kudurin nasu wata ilhama ce aka kimsawa jam’iyyar ta JMPP, ya jaddada cewa sauya sunan Najeriya da kudinta ya zama tilas muddin ana so kasar ta ci gaba.

A cewar Ijagbemi, idan sukai nasarar lashe zabukan 2019, zasu sauya sunan Najeriya zuwa Pisonia, kudin kasar kuma zai koma amsa sunan Pison a maimakon Naira, zalika, za su kuma gudanar da gagarumin aikin zagayen kasar ta Najeriya da Katanga, domin sa ido sosai kan mutanen da shiga da fita kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.