Isa ga babban shafi
Najeriya

"Hare-haren 'yan bindiga ya lakume naira biliyan 17 a Zamfara"

Gwamantin jihar Zamfara a Najeriya, ta ce akalla mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da barayi da ‘yan fashi ke kai wa jama’a, yayin da lamarin ya yi sanadiyyar asarar dukiya mai yawan gaske.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari. RFIHAUSA
Talla

Kafafen yada labaran Najeriya sun rawaito Sakataren gwamnatin jihar ta Zamfara Farfesa Abdullahi Shinkafi na cewa, barayin sun lalata gidaje sama da dubu 2, tare da kone motoci akalla 500.

Shinkafi ya kara da cewa, barayin sun kuma yi garkuwa da mutane sama da 500 domin neman kudaden fansa.

Sakataren gwamnatin ta Zamfara, ya ce jimillar kudaden da matsalar fama da hare-haren ‘yan bindigar ta lakumewa jihar ta Zamfara ya kai akalla naira biliyan 17, daga shekarar 2011 zuwa yanzu.

A cewar jami’in kudaden sun kunshi na sayawa hukumomin tsaro sabbin motoci, da yawansu ya haura 300, daga 2011 zuwa 2018, sai kuma biyan jami’an tsaron kudaden alawus, da gina muhalli ga sojojin Najeriya da ke bataliya ta 232 wadanda ke samar da tsaro a jiha ta Zamfara, bayaga sauran al’amuran bukatu na kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.