Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kai hari kauyuka 5 na Zamfara tare da kashe mutane 6

Wani sabon harin ‘yan bindiga kan kauyuka 5 na arewacin jihar Zamfara a Tarayyar Najeriya ya hallaka akalla mutane shida tare da jikka wasu da dama, baya ga kwashe tarin dabbobi.

Tuni dai daruruwan al'ummar kauyukan suka kauracewa gidajensu don tsira da rayukansu.
Tuni dai daruruwan al'ummar kauyukan suka kauracewa gidajensu don tsira da rayukansu. rfihausa
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar wadanda suka farmaki kauyukan Hayin Alhaji da Totari da Nawaje da Bawo da kuma Bantsa sun yi awon gaba da tarin duniya, yayinda suka ci zarafin wasu tarin mata ta hanyar yi musu fyade bayan kashe mazajensu.

Wani mazaunin jihar ta Zamafara Bala Yaro Mada ya tabbatar mana da cewa yanzu haka akwai tarin jama’a da suka kauracewa kauyukan biyar bayan harin na daren Juma’a wayewar Asabar da kuma na daren Alhamis wayewar jiya Juma’a.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren 'yan bindiga wanda ya faro daga satar shanu ya juye zuwa garkuwa da mutane don kudin fansa yanzu kuma ya koma hare-haren kisa tare da kwashe tarin dunkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.