Isa ga babban shafi
Najeriya

Malaman jami’oin Najeriya sun gindaya sharuddan janye yajin aiki

Kungiyar malaman jami’o'in Najeriya ASUU, ta gindaya sharuddan janye yakin aikin da 'ya'yanta suke yi na sama da watanni biyu, inda ta bukaci gwamnatin kasar ta basu naira biliyan 50.

Wasu daliban Jami'a a Najeriya
Wasu daliban Jami'a a Najeriya Reuters
Talla

Shugaban malaman jami'o'in Biodun Ogunyemi, yace naira biliyan 50 da suke nema zai zama wani kashi ne na naira biliyan 220 da suke bukata daga hannun gwamnati domin inganta ayyukan manyan makarantun.

Ogunyemi yace a shirye suke su janye yajin aikin muddin gwamnatin ta biya wadannan bukatu.

Ranar 5 ga watan Nuwamban da ya gabata, malaman jami’o’in Najeriyar suka soma yajin aiki, kan wasu bukatu da dama, wadanda ke kunshe cikin yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar a shekarar 2009.

Wasu daga cikin bukatun sun hada da neman kara yawan kudaden gudanarwa da gwamnati ke baiwa jam’o’in tarayya, da kuma tabbatar da cewa ana baiwa jami’o’i mallakar jihohi isassun kudaden bunkasa su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.