Isa ga babban shafi
Najeriya

Ubangiji ne kawai zai iya dakatar da zabukan 2019 - INEC

Hukumar shirya zaben Najeriya INEC, ta bayyana kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zabukan kasar, a ranar Asabar da ke tafe, inda za a soma da na shugaban kasa da na majalisun dattijai da wakilai.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Yakubu Mahmood.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Yakubu Mahmood. KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images
Talla

Yayin da yake yiwa tawagar jami’an sa ido kan zabukan Najeriyar na ciki da wajen kasar da sauran masu ruwa da tsaki jawabi, kwamishin INEC na kasa dakta Mustapha Lecky, da ya wakilci shugaban hukumar Farfesa Mahmaood Yakubu, ya ce Allah ne kawai ke da ikon dakatar da zabukan kasar da aka shirya za su gudana.

A cewar shugaban na INEC, a halin yanzu babu wani dalili da zai hana hukumar gudanar da zabukan kamar yadda aka tsara, la’akari da kwararan matakan da suka dauka na tabbatar da cewa komai ya tafi dai dai.

Hukumar INEC, ta kuma jaddada matsayinta na fatan gudanar da zabe mafi tsafta a tarihin Najeriya.

Yayin da ya ke tsokaci, ministan harkokin wajen kasar, Geoffery Onyema, ya bukaci kasashen duniya su mutunta ‘yancin Najeriya, su kuma kaucewa yi mata katsalandan a harkokinta na cikin gida, inda yayi gargadin cewa, kasar ba za ta yadda da kutse cikin al’amuranta ba bisa ka’ida ko gayyata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.