Isa ga babban shafi
Najeriya

2019: Buhari da Atiku sun kada kuri'a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC tare da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP sun bi ayarin sauran ‘yan Najeriya wajen kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisun dattijai da na wakilai a yau Asabar.

Nigeria President, Muhammadu Buhari of APC and his main challenger casting their votes during Sartuday's Presidential election. 23/02/2019.
Nigeria President, Muhammadu Buhari of APC and his main challenger casting their votes during Sartuday's Presidential election. 23/02/2019. RFIHAUSA
Talla

Shugaba Buhari ya kada kuri’arsa ce da misalin karfe 8 na safiyar wannan Asabar a mahaifarsa garin Daura da ke jihar Katsina, yayinda babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya kada tasa kuri’ar a Jada da ke jihar Adamawa da misalign karfe 10 na safiya a yau Asabar.

Abokan hamayyar biyu da suka taba kasancewa tare a jam’iyyar APC, sune kan gaba tsakanin ‘yan takara 73 da ke neman darewa kujerar shugabancin Najeriyar, kasa mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Hukumar shirya zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, ta ce ‘yan kasar miliyan 72 da dubu 8 suka cancanci kada kuri’a a zabukan kasar na 2019, bayan karbar katunansu na din-din-din.

Yayin da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun wakilai da dattijan kasar ke gudana; a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya, rahotanni sun ce daruruwan mazauna kauyen Geidam da ke jihar Yobe sun tsere daga muhallansu, sakamakon farmakin da wasu gungun mayakan Boko Haram suka kai musu.

Harin ya zo kwana guda bayan da dakarun sojin Najeriya suka dakile harin da wasu mayakan na Boko Haram suka kai garin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno a ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.