Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 233 sun mutu a rikice-rikicen zaben Najeriya

Wata Cibiyar Bincike Mai Zaman Kanta SBM, ta bayyana cewa, mutane 233 ne suka rasa rayukansu a wasu rikice-rikicen siyasa da suka wakana tsakanin watan Oktoban bara zuwa Juma’ar da ta gaba a Najeriya.

Ana zargin 'yan bangar siyasa da kashe jama'a a yayin gangamin siyasa a Najeriya
Ana zargin 'yan bangar siyasa da kashe jama'a a yayin gangamin siyasa a Najeriya guardian.ng
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu 'yan bindiga suka kashe wani jigo a jam’iyyar APC a karamar hukumar Andoni da ke jihar Rivers a kudancin Najeriya, a daidai lokacin da jama’a suka shagala wajen kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da ke gudana a wannan Asabar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Sernibo Finebone, ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bangar siyasar PDP ne suka kashe Cif Mowan Etete da ya kasance mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar, sannan kuma ya rike mukamin shugaban karamar hukumar a can baya.

Har ila yau akwai, wasu mutane uku da suka hada da dan uwan Mr. Etefe da su ma suka rasa rayukansu sakamakon bude wutar da ‘yan bangar siyasar suka yi .

Jami’an 'yan sanda sun ce, an kuma sace kayayyakin zabe a wasu wurare a  jihar ta Rivers duk da kashedin da gwamnatin kasar ta yi kan sace kayan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.