Isa ga babban shafi

Fadar Najeriya ta nesanta Buhari da hannu a kudirin kara wa'adin mulki

Fadar mulkin Najeriya ta fitar da sanarwar da ke nesanta shugaba Muhammadu Buhari da hannu wajen gabatar da kudirin da ke shirin mayar da tsarin kowanne wa’adi na mulkin kasar zuwa shekaru 6, kudirin da ya sha kaye a gaban majalisun kasar cikin makon jiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo dailypost.ng
Talla

Cikin sanarwar fadar ta bayyana cewa guda cikin ‘yan Majalisar wakilai da ta kira sunanshi da Mr John Dyegh ne ya gabatarwa Majalisar kudirin, kuma ko da majalisar ta aminta da kudirin ba zai fara aiki ba sai bayan gushewar gwamnati mai ci shekarar 2023.

A cewar babban mataimaki na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari kan al’amuran da suka shafi Majalisa Senator Babajide Omoworare, ya bayyana cewa shugaban Najeriyar ya sha nanata rashin bukatar shi ta kara koda kwana guda a mulki bayan karewar wa’adinsa, hasalima ya sha alwashin kin mara baya ga kowanne dan siyasa yayin zaben shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.