Isa ga babban shafi
Najeriya - Kebbi

Kebbi: An tsamo gawarwakin mutane 76 da jirginsu ya nutse a kogi

Jami’an ceto a Jihar Kebbi dake Najeriya sun samu nasarar tsamo gawarwaki 76 na fasinjojin jirgin ruwan da ya nutse a kogi.

Masu aikin ceto a Kebbi bayan kifewar wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji kusan 200.
Masu aikin ceto a Kebbi bayan kifewar wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji kusan 200. AFP - -
Talla

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, manajan hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya a yankin Jihar Kebbi Yusuf Birma Shalbwala ya ce sun samu nasarar tsamo gawa 76 ne ya zuwa jiya Juma’a.

Ana fargabar adadin mutanen da suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin ruwan a ranar Laraba ya kai akalla 160, yayin da kuma aka samu nasarar ceto mutane 22 da ransu.

Jirgin ya taso ne daga jihar Neja, inda ya doshi jihar Kebbi, yana tsaka da tafiya ne kuma ya rabe gida biyu kafin ya nutse  kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.

Bayanai sun ce, jirgin ruwan yayi dakon fasinjoji akalla kusan 200 ne da kuma kayayyakin da suka wuce kima, ganin cewa, mutane 80 kadai jirgin ke iya dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.