Isa ga babban shafi
NAJERIYA-CIN HANCI

Yaki da cin hanci na da wahala - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa da yayi alkawarin aiwatarwa domin kwato kudaden hukuma na da matukar wahala a karkashin mulkin farar hula.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Twitter / @MBuhari
Talla

Buhari yace yana fuskantar matsaloli sosai wajen yaki da cin hancin tunda ya hau karagar mulki a shekarar 2015 saboda yadda tsarin ke tafiya da kuma yadda ake gudanar da shari’u a kotuna domin hukunta wadanda ake tuhuma, sabanin lokacin da yayi mulkin soji a shekarun 1980.

Shugaban yace duk da haka gwamnatin sa tayi nasarar yakin a wasu bangarori duk da yake bata shelanta shi domin Yan Najeriya su fahimci abinda ke tafiya.

A wata hira ta musamman da yayi da tashar Arise TV da aka watsa yau alhamis, shugaban ya bayyana matukar damuwar sa da yadda Gwamnonin jihohi ke tafiyar da kananan hukumomi wadanda yanzu haka yace an hana su aiki.

Buhari yayi misali da yadda wasu gwamnonin ke hana kananan hukumomi kudaden da ake basu daga asusun tarayya, inda yake cewa idan an baiwa karamar hukuma naira miliyan 300 sai gwamna ya karbe miliyan 200 ya baiwa shugaban karamar hukuma naira miliyan 100 yayi aiki da shi.

Kokarin Buhari na baiwa kananan hukumomin kasar damar cin gashin kan su kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada ya gamu da rashin amincewa daga gwamnonin wadanda suka yi watsi da shi.

Dangane da Yan bindiga kuma da masu garkuwa da mutane da suka addabi Yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, shugaban kasar yace ya baiwa sojoji da yan sanda umurnin cewar babu sani babu sabo kan duk masu daukar makamai suna razana jama’ar kasa daga kowanne sashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.