Isa ga babban shafi
NAJERIYA-KIWO

Zamu kwato burtalolin da jama'a suka mamaye - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana shirin gwamnatin sa na kwato burtaloli da gandun dajin da mutane suka mamaye abinda ke haifar da rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma wanda ke kaiga rasa dimbin rayuka.

Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna.
Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna. AFP/Getty Images - Stefan Heunis
Talla

Shugaba Muhammadu Buhari yace ya baiwa ministan shari’ar kasar Abubakar Malami umurnin amfani da dokokin kasa wajen karbo wadannan burtiloli da kuma gandun dajin da aka ware domin kiwo aka kuma yi doka akan su daga hannun wadanda suka mamaye su wajen yin gonaki ko gidaje.

Shugaban yace bisa ka’ida Fulani makiyaya na amfani da wadannan burtiloli wajen tafiye tafiye da dabbobin su domin kaisu inda za’a suyi kiwo matakin da ke kare su daga fadawa gonaki ko filayen jama’a wanda ke haifar da tashin hankali.

Buhari yace lokacin da ake amfani da wadannan burtiloli duk makiyayin da ya bari shanun sa suka shiga gonakin manoma akan kai su gaban hukumomin yankin ko ofishin Yan Sanda domin ganin sun biya diyya sabanin yadda ake gani ayau na samun tashin hankalin dake kaiga rasa rayuka.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya dauki wani sabon salo a Najeriya inda ake samun rasa dimbin rayuka a jihohin kasar da dama, abinda ya sa jihohin dake yankin kudancin kasar da kuma wasu daga bangaren arewa suka haramta yawon da Fulani makiyaya keyi suna kiwon dabbobin su baki daya.

Daukar wannan mataki na hana yawon kiwon ya gamu da suka daga wasu sassan jama’ar kasar amma masana harkar kula da dabbobi sun bada shawarar cewar lokaci yayi da za’a rungumi dabarun zamani wajen inganta harkar makiyayan sabanin wanda ake gudanarwa shekara da shekaru.

Daga cikin masu irin wannan ra’ayi harda tsohon Gwamnan Jihar Adamawa kuma hamshakin manomi Murtala Nyako wanda yace banda wahala babu abinda makiyayan ke sha wajen yawo da dabbobin su.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bullo da shirye shiryen da suka hada da na Ruga da kuma shirin inganta kiwo na ‘National Livestock Project’ amma siyasa ta sanya wasu al’ummar kasar adawa da shirin baki daya.

Kungiyar 'International Crisis Group' dake da Cibiya a Paris wadda ke nazarin rikice rikice a kasashe masu tasowa tace abin takaici ne duk da ingancin tsarin shirin na gwamnatin tarayya siyasa da rashin fadakar da jama’ar da zasu amfana da shi ya sa an gaza wajen aiwatar da shi kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.