Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Ba zamu bar 'yan siyasa su jefa Gombe cikin tashin hankali ba - Yahaya

Gwamnan Jihar Gombe dake Najeriya Inuwa Yahaya yace bincike ne kawai zai tabbatar abinda ya faru lokacin da wasu matasa suka tare tsohon Gwamna Sanata Danjuma Goje akan hanyar sa ta shiga garin Gombe a makon jiya.

Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya
Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya © RFI Hausa
Talla

Yahaya yace tunda Sanata Goje ya gabatar da korafi a ofishin ministan shari’a Abubakar Malami da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Alkali Baba da ministan ‘Yan Sanda Maigari Dingyadi da kuma ofishin kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, ya dace a saurara domin jin abinda bincike zai nuna.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da Sanata Goje ya gabatarwa manema labarai ta hannun Lilian Nworie, cewar magoya bayan Gwamna Yahaya sun kai masa hari lokacin da ya ziyarci jihar domin halartar bikin daurin aure, inda yace ana barazana ga rayuwar sa.

Gwamnan wanda ya zargi Sanata Goje da kokarin haifar da tashin hankali, yace mutanen jihar sun ki yarda da shirin sa, amma hakan bai hana samun arangamar da ta kai ga rasa rayuka da lalata dukiyoyi ba.

Tsohon Gwamnan Jahar Gombe Danjuma Goje
Tsohon Gwamnan Jahar Gombe Danjuma Goje @Next

Yahaya ya bayyana cewar ana ci gaba da zaman lafiya a Jihar sa, yayin da jama’a ke gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da tsangwama ba, a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke gudanar da binciken su.

Gwamnan wanda ya bayyana Sanata Goje a matsayin dattijon da ya dace ya dinga hana masu shirin tada hankali amma ba masu tinzira ta ba saboda neman biyan bukatar kan su, yace gwamnatin sa ba zata amince da duk wani yunkurin tada hankalin jama’a ba.

Dangane da rade radin da ake cewar, barakar da ta kunno kai a tsakanin su na da nasaba da zaben shekarar 2023, Gwamna Yahya yace Ubangiji ne kawai ya san wanda zai rayu zuwa shekarar 2023 tsakanin shi da Sanatan, yayin da yayi watsi da zargin cewar gwamnatin sa ta karbe ragamar jam’iyyar su ta APC a Jihar.

Shugaban Jam'iyyar APC na riko Mai-Mala-Buni
Shugaban Jam'iyyar APC na riko Mai-Mala-Buni © Daily Nigerian

Masu sanya ido a siyasar jihar na bayyana damuwa akan barakar da kunno kai tsakanin jiga jigan ‘Yan siyasar, wadanda ke da karfin fada aji a siyasar Gombe da kuma ta kasa baki daya.

Yunkurin karbe iko da jam’iyyar APC ya bar baya da kura a jihohin Najeriya da dama, abinda ya nuna yadda aka samu shugabannin Jam’iyyar 92 a matakin jihohi 36 lokacin da aka gudanar da tarukan jam’iyyar na jihohi a watan jiya.

Wannan ya sa sabon shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya yiwa APC shagube bayan nasarar zaben da ya samu, inda yace ba Jam’iyyar ba zata iya gudanar da taron kasa domin zaben shugabannin ta kamar yadda PDP tayi ba, saboda tarin matsalolin da suka kunno kai a matakan jam’iyyar na jihohi, abinda ya ce ya kama hanyar rugujewar jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.