Isa ga babban shafi
Najeriya

Hadarin kwale-kwale ya hallaka mutane 18 a Katsina

Akalla Mutane 18 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani hadarin kwale kwale a Jihar Katsina dake Najeriya, yayin da wasu kuma suka bata.

Wani kwale-kwale dauke da jama'a a Ubangui
Wani kwale-kwale dauke da jama'a a Ubangui ISSOUF SANOGO/AFP
Talla

Wani mazaunin Yankin Lawal Sakatare ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar mutane 24 ke cikin kwale kwalen lokacin hadarin, yayin da ake bikin Sallah, kuma an gano gawarwakin 18 daga cikin su, kuma akasarin su yara ne.

Sakatare yace 14 daga cikin su sun fito ne daga kauyen Tsabu, 4 daga Dogon Hawa, kuma tuni akayi janaizar 15 daga ciki su a Mai’adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.