Isa ga babban shafi

Najeriya ba za ta tsoma baki a shari’ar Sanata Ike Ekweremadu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba za ta tsoma baki a shari’ar da ake yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu a birnin Landan na kasar Birtaniya ba.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu. PHILIP OJISUA/AFP/Getty Images
Talla

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya bayyana haka ya yi wani taron manema labarai a fadar gwamnati, dake Abuja a ranar Alhamis ya ce gwamnatin Najeriya na da al'adar rashin tsoma baki a duk wani lamari na shari'a na gida ko na waje.

Wannan matsayi, a cewarsa, zai ci gaba da tsayawa kan lamarin da ya shafi tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a shari’ar da ake yi masa a kotun Burtaniya.

Da aka tambaye shi kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sa baki a shari’ar da ta shafi Sanata mai wakiltar Enugu ta Yamma a Majalisar Dokoki ta kasa dangane da shari’ar da ake yi masa a Birtaniya, Malami ya ce, “Bai  taba zama al’adar gwamnatin Najeriya ta tsoma baki kan wani abu na shari’a  na gida ko na waje. Kuma wannan shine matsayin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.