Isa ga babban shafi

Najeriya da Faransa sun kulla yarjejeniyar samar da wadataccen lantarki

Gwamnatin Najeriya da hukumar raya kasashe ta Faransa AFD sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da hasken lantarki a yankin arewacin Najeriya, aikin da zai lakume Euro miliyan 25. Hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai da kuma hukumar AFD ta Faransa ne zai samar da kudaden aikin samar da lantarkin.

Tsawon shekaru Najeriya na fama da matsalar karancin lantarki duk da makuden kudaden da kasar ta kashe a fannin.
Tsawon shekaru Najeriya na fama da matsalar karancin lantarki duk da makuden kudaden da kasar ta kashe a fannin. REUTERS - CARLOS GARCIA RAWLINS
Talla

Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Clem Agba da daraktan hukumar raya kasashe ta Faransa a Najeriya Xavier Muron ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar ranar Laraba a gaban jakadan Faransa dake Najeriya Emmanuelle Blatmann da shugaban tawagar kungiyar kasashen Turai a Najeriya da kungiyar ECOWAS, Cecile Tassin-Pelzer.

Aikin samar da lantarkin a arewacin Najeriyar dake karkashin kamfanin samar da lantarki na kasar (TCN), na da nufin bunkasar karfin tattalin arziki maras dogaro da fitar da gurbatacciyar iska a Afirka ta Yamma, ta hanyar inganta layukan rarrabar wutar lantarki a Najeriya tare da tallafawa ci gaban kasuwar hasken lantarki a tsakanin kasashen yankin yammacin Afirka.

Daga cikin manyan muradun da wannan gagarumin aiki ya sanya a gaba akwai, taimakawa wajen rarraba wutar lantarkin da ake samu daga rana a karkashin ayyukan inganta karfin lantarkin da za a yi nan gaba a rewacin Najeriya.

Sai kuma gina layukan rarraba lantarkin da tsawonsu ya zarce kilomita fiye da 800, tare da ginawa ko habaka tashoshin wutar 13.

Kididdiga ta nuna cewar jimillar kudaden da wanna katafaren aikin zai lakume ya kai kusan Yuro miliyan 238, idan aka hada da yarjejeniyar gudunmawar euro miliyan 202 da hukumar raya kasashe ta Faransa ta rattabawa hannu a watan Disambar shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.