Isa ga babban shafi

Nijar da Bankin Duniya sun cimma yarjejeniyar samar da lantarki

Ma'aikatar Makamashi a Jamhuriyar Nijar ta sanar da cimma matsaya tsakaninta da Bankin duniya karkashin wani shiri da zai samar da lantarki ga kimanin kashi 30 cikin dari na al’ummar kasar nan da shekarar 2026, bisa manufar kai wa kashi 80 nan da shekarar 2035, sabanin kashi 17.5% da ake da shi a yanzu.

Shirin zai samar da kashi 80 na lantarki nan da shekaru 25 masu zuwa.
Shirin zai samar da kashi 80 na lantarki nan da shekaru 25 masu zuwa. © Stephane Mahe/Reuters
Talla

Jumullar kudin da suka kai miliyan 317 na dalar Amruka ne wannan shiri da aka yi wa lakabi da haske zai lakume, bisa manufar da ake da ita na samar da wutar lantarkin ga al’ummar da ke cikin karkarun kasar, ma’aikatun kiyon lafiya da samar da ilimi da kuma ga kafanoni da masana’antu kamar yadda ministan makamashin Ibrahim Yacoubou, ya sanar a lokacin bikin kaddamar da shirin a jiya talata.

Har ila yau shidai wannan shiri na Haske ya tanadi fadada aikin samar da makamashin wutar lantarki ta hasken rana a cikin  wannan  katafariyar kasa dake kunshe da sama da al’ummaa miliyan 22.

Yanzu haka dai a jamhuriyar Nijer, ita ce ne ke samar da kimanin kashi 80%" na makamashin da magidanta ke amfani da shi wajen girki, duk da cewa kashi 2 bisa 3 na fadin kasar ya kasance Hamada, da kuma ke fama da matsalolin daban daban da sauyin yanayi ya haifar.

Domin ganin ta rage dogaron da take yi da makwabciyarta tarayyar Najeriya dake sayar mata kashi (70%) na makamashin wutar lantarkin ne, jamhuriyar ta matsa kaimi wajen ganin ta kammala gina madatsar ruwanta ta farko  da take yi kan kogin Nijer nan da  2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.