Isa ga babban shafi

Najeriya: PDP ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa ba da taimako na ba - Wike

A Najeriya, yayin da Jam’iyyar PDP ke ci gaba da kokarin dinke barakar dake cikin ta domin tinkarar zabe mai zuwa, Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike yace babu yadda za’ayi Jam’iyyar ta lashe zaben shugaban kasa mai zuwa ba tare da sanya hannunsa a ciki ba.

Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike
Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike © Nyesome Wike
Talla

Gwamnan ya shaidawa manema labarai cewar ya zama dole a saurare shi tare da wasu gwamnoni guda 4 da suka kauracewa jam’iyyar domin biya musu bukatarsu na sauke shugaban ta Iyorchia Ayu daga kujerarsa.

Cin amana

Wike yace Jam’iyyar PDP ta ci amanarsu wajen kin mutunta dokokin ta na raba daidai dangane da abinda ya shafi mukamai, saboda haka suke bukatar shugaban jam’iyyar ya sauka daga kujerarsa domin mayar da ita kudu, tunda dan takaran shugaban kasa ya fito daga yankin arewa.

Gwamnan yace wannan dalili ne kawai zai sanya su goyi bayan Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

Kokarin Jam’iyyar na sasantawa da Wike wajen ganin ya sassauta matsayinsa ta hanyar shirya taro tsakaninsa da Atiku da kuma tura masa tawagogin manyan ‘yan jam’iyar domin bashi baki yaci tura.

Ganawa a Spain

Yanzu haka rahotanni sun ce Wike da abokan tafiyarsa wasu gwamnoni guda 4 da suka hada da Samuel Ortom na Benue da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na Abia da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu na kasar Spain inda akace suna gudanar da wani taro akan rikicin jam’iyyar ta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.