Isa ga babban shafi

Sabon gwamnan Osun ya kori ma'aikata dubu 12 da sarakuna uku

Jam’iyyar APC da Majalisar Dokokin Jihar Osun dake Najeriya sun yi tir da matakin sabon Gwamnan Jihar, Ademola Adeleke, kan wasu Dokokin Zartarwa guda shida da ya sanya wa hannu a ranar Litinin.

Sabon gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke yayin karbar ragamar jagorancin jihar 27/11/22.
Sabon gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke yayin karbar ragamar jagorancin jihar 27/11/22. © Ademola Adeleke
Talla

Sun yi Allah-wadai da matakin sabon gwamnan kan sauya wasu nade-nade da daukar ma'aikata da magabacinsa Gboyega Oyetola ya yi a baya.

Kokarar ma'aikata

Matakin farko da Adeleke ya dauka amatsayinsa na gwamna da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP ya sanar da korar ma’aikata 12,000 da ake zargin magajinsa ya dauka aiki.

Ya kuma sauke wasu sarakuna uku da kuma umarnin janye takardar shaidar nasarar zaben shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta gudanar a ranar 15 ga watan Oktoba.

Zaben kananan hukumomi

Matakin janye shedar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren Hukumar zaben jihar OSIEC, Adedapo Adejumo, a Osogbo ranar Litinin.

Tun da farko dai sakataren gwamnatin jihar Tesleem Igbalaye ya sanar da dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun Mista Segun Oladitan tare da wasu mambobin hukumar guda shida matakin da ya fara aiki nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.