Isa ga babban shafi

Da na so zan iya neman wa'adi na 3 a 2007- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa idan da ya so zai iya ci gaba da mulkin kasar duk da karewar wa’adin mulkinsa a shekarar 2007.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

A cewar Obasanjo ya na da cikakkiyar damar iya ci gaba da mulki a wa’adi na 3 amma sam ba shi da sha’awar tsawaita mulkinsa dalilin kenan da ya sanya shi sauka a wancan lokaci.

Yayin jawabinsa a wani taro da wata kungiya mai rajin tabbatar da shugabanci nagari a nahiyar Afrika ta shirya, tsohon shugaban na Najeriya ya musanta jita-jitar da ta karade kasar a wancan lokaci na cewa ya so ya ci gaba da mulki a wa’adi na 3, yana mai cewa ko shakka babu idan har da ya so hakan to da wani zance ake yi ba wannan ba.

Akwai dai jita-jitar da ke cewa Olusegun Obasanjo ya bukaci ci gaba da mulkin Najeriya bayan karewar wa’adinsa a 2007 amma kuma ya fuskanci tirjiya dalilin da ya kai ga zaben Marigayi Alhaji Umaru Musa ‘yar Adua a wancan lokaci.

Obasanjo wanda a baya-bayan nan ya fito fili ya goyi bayan dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar LP wato Peter Obi ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen gamsar da ‘yan Najeriya don ganin sun juyawa jam’iyyun PDP da APC baya a zaben da ke tunkarowa cikin watan gobe.

Olusegun Obasanjo wanda ya nesanta kansa da zamowa mamba wata jam’iyyar siyasa a Najeriya, ya roki matasan Najeriya su kaucewa tafka kuskure yayin zaben na bana yana mai cewa yana da yakinin Obi zai kawo ci gaba da maslaha a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.