Isa ga babban shafi

'Yan Najeriya miliyan 94 na kada kuri'a don zaben sabon shugaban kasa

Yau ‘yan Najeriya sama da miliyan 93 ke fita rumfunan zabe a Jihohi 36 da kuma Abuja domin kada kuri’a ga wanda zai gaji shugaban kasar Muhammadu Buhari da ke kawo karshen wa’adin mulkinsa a wannan shekara bayan kwashe shekaru 8 a karagar mulki. 

Wasu 'yan Najeriya a jihar Kano sun layi domin kada kuri'ar su a zaben shugaban kasa. 25/02/2023.
Wasu 'yan Najeriya a jihar Kano sun layi domin kada kuri'ar su a zaben shugaban kasa. 25/02/2023. © Amélie Tulet/RFI
Talla

‘yan takara 18 zasu fafata domin neman shugabancin, kuma daga cikinsu ana ganin Atiku Abubakar mai shekaru 76 daga Jam’iyyar PDP da Bola Ahmed Tinubu mai shekaru 70 na Jam’iyyar APC da Peter Obi mai shekaru 61 na Jam’iyyar Labour baya ga Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP su ke kan gaba wajen yiwuwar iya lashe zaben na yau. 

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce dokar da ake amfani da ita ta bayyana cewar wanda zai samu nasara sai ya samu kuri’u mafi yawa da kuma samun kashi 25 na yawan kuri’un da aka kada a kashi biyu bisa 3 na jihohi 36 da ake da su da kuma Abuja fadar gwamnatin kasar. 

Idan babu wani ‘dan takarar da ya samu wannan adadi daga cikin mutane 18 da ke neman shugabancin, Hukumar zabe ta ce dole a je zagaye na biyu na zaben bayan kwanaki 21 tsakanin ‘yan takara guda biyu da suka fi yawan kuri’u.

Hukumar zaben ta gabatar da wasu sabbin na’urorin zamani da za ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben da ake kira BVAS wadanda za su taimaka wajen inganta sahihancin zaben. 

Zaben na Najeriya a wannan karon na zuwa ne a wani yanayi da al'ummar kasar ke fama da kuncin rayuwa musamman bayan matakin sauya fasalin takardaun kudin da ya haddasa karancin tsabar kudi a hannun jama'a.

Bugu da kari a bangare guda, matsalolin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane ya sanya fargabar yiwuwar ganin karancin fitowar jama'a don kada kuri'a a zaben na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.