Isa ga babban shafi

Amurka ta taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben Najeriya

Amurka ta taya zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben kasar da ya gudana a karshen makon da ya gabata, yayinda ta yi kira da a kwantar da hankula duk da zarge-zargen magudin zabe da kuma tangardar na’urar da aka samu a wasu yankuna.

Shugaba Joe Biden na Amurka.
Shugaba Joe Biden na Amurka. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayin ganawarsa da ministan wajen Najeriya Geoffrey Onyeama yau alhamis a wani bangare na taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da ke gudana a New Delhi.

Tun a jiya laraba ne ma’aikatar wajen Amurka ta taya Tinubu murnar lashe zaben Najeriyar mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika da ya gudana ranar 25 ga watan Fabarairu.

A cewar kakakin ma’aikatar wajen na Amurkan Ned Price, sakamakon zaben ya bude sabon babi ga siyasa da Demokradiyyar Najeriya.

Mr Price ya ci gaba da cewa jam’iyyun adawa na da damar kalubalantar yadda yanayin bayyana sakamakon zaben ya tafi da kuma yadda aka gudanar da shi a wasu yankuna, amma akwai bukatar bin matakan shari’a don wannan bore maimakon tayar da hankula.

Sakamakon zaben na ranar asabar dai da hukumar INEC ta sanar karkashin jagorancin Farfesan Mahmud Yakubu ya nuna yadda Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ya samu kuri’u miliyan 8 da dubu dari 8 da ‘yan doriya yayinda Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ke biye da shi da yawan kuri’u miliyan 6 da dubu dari 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.