Isa ga babban shafi

Bazoum na Nijar ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben Najeriya

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da ya lashe zaben kasar na ranar asabar din da ta gabata.

Mohamed Bazoum, na jamhuriyyar Nijar.
Mohamed Bazoum, na jamhuriyyar Nijar. © Bertrand Guay / AFP
Talla

Wata wasika da Bazoum ya aikewa Bola Tinubu ta ruwaito shugaban na Nijar na bayyana gamsuwa da sahihancin zaben Najeriya wanda ya ce jigo ne ga dorewar demokradiyya a nahiyar Afrika.

Bazoum ya ci gaba da cewa ‘‘ Ni da al’ummar Nijar da na ke wakilta muna mika sakon fatan alkhairi ga makwabtanmu al’ummar Najeriya tare da fatan tabbatar zaman lafiya da habakar tattalin arziki a kasar’’

A cewar shugaban na Nijar Bazoum Mohamed abin alfahari ne yadda Najeriya ta girmama dekmokradiyya wajen bayar da cikakkiyar dam aga ‘yan kasar wajen zaben son ransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.