Isa ga babban shafi

Yadda kalaman tunzuri ke neman kawo cikas ga zabukan Najeriya

A Najeriya Rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto ta bayyana cewar kalaman tunzura jama’a da wasu ‘yan siyasa ke yi na iya kawo tashin hankali lura da wani abin da ya ja hankali a bayan nan na zazzafan kalamai da aka ji suna fitowa daga bakunan manyan ‘yan siyasa a jihar. 

Wasu masu kada kuri'u yayin zaben shugaban kasa Najeriya na 2015.
Wasu masu kada kuri'u yayin zaben shugaban kasa Najeriya na 2015. © AP
Talla

Wannan na zuwa kusan makonni biyu kenan da aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a sassan kasar, wanda Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben.

Hukumomi dai a kasar sun sha alwashin daukar tsauraran matakai kan duk dan siyasar da ssuka ssamu a kasar yana yunkurin tayar da zaune tsaye, ko kuma yada kalaman tunzura jama'a.

Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken rahoton da Faruk Muhammad Yabo ya hada kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.