Isa ga babban shafi

Ku karbi kudinsu ku zabi abinda kuke so - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su karbi kudaden da 'yan siyasa suke rabawa lokacin zabe, amma kuma su zabi abinda suke so. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AP - Christophe Ena
Talla

Yayin da yake jawabi ga manem alabarai bayan kada kuri’ar sa a zaben gwamnan jihar Katsina da na ‘yan majalisu, shugaban ya ce yana da yakinin jam’iyyarsa ta APC za ta sake samun nasara. 

Shugaban ya ce ko kadan bai yi mamakin yadda sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu ya kaya ba, wanda aka bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara. 

Buhari ya ce Jam’iyyar APC ta gudanar da yakin neman zabe tukuru wajen bayyana manufofinta da shirin da take da shi ga jama’ar Najeriya. 

Shugaban yace duk da yadda matsalar karancin kudi ta yiwa shirin sayen kuri’u dabaibayi, har yanzu wasu bata garin ‘yan siyasa na rabawa masu zabe kudade. 

Buhari ya bai wa jama’a shawarar cewar su karbi kudinsu soke, kana su zabi abinda suke so. 

Daga karshe shugaban ya jinjinawa ‘yan Najeriya akan amincewar da suka yi wa jam’iyyar su, yayin da su kuma suka saka musu wajen gudanar da ayyuka a bangaren ilimi da kula da lafiya da kuma gina kayan more rayuwa. 

Shugaban ya kuma yabawa kafofin yada labarai saboda rawar da suka taka wajen wayar da kan jama’a domin zabin irin shugabannin da suke so da kuma tuhumarsu idan sun saba alkawarin da suka musu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.