Isa ga babban shafi

Mutane sun kare kuri'unsu na zaben gwamna a wasu sassan Najeriya

Yayin da aka fara bayyana sakamakon zaben wasu kananan hukumomi a sassan jihohin Najeriya, al’umma na ci gaba da sanya idanu don tabbatar da ganin wanda suka zaba shi ne ya kai ga nasara. 

Wasu matasa yayin wasa jam'iyyyar da suke goyon baya a jihar Kano da ke Najeriya.
Wasu matasa yayin wasa jam'iyyyar da suke goyon baya a jihar Kano da ke Najeriya. AP - Sani Maikatanga
Talla

Sai dai zaben na gwamna ya sha ban-ban da na shugaban kasa, ta fannin tsaro, la’akari da yadda na gwamna ya gamu da matsalolin hare-haren ‘yan bangar siyasa da kuma yunkurin harin ‘yan ta’adda. 

Misalin yankunan da aka sami tashin hankali, sun hada da sassa da dama na jihar Lagos, inda ‘yan bangar siyasa suka rika kai wa runfunan zabe hari, tare da tarwatsa masu zaben. 

Haka abin yake a jihar Kano, inda dama tun kafin lokacin zaben ya zo aka yi hasashen faruwar rikici, la’akari da yadda karfin manyan jam’iyyun da ke kan gaba ya kusan zuwa daya. 

A Kanon dai, an hango yadda mazabu da dama suka hadu da tsautsayin ‘yan bangar siyasa da ke yunkurin tayar da tarzoma musamman guraren da suka fuskanci ‘yan takarar su na shan kaye. 

Sai dai a iya cewa kan masu zabe ya fara wayewa, duba da yadda matasan wasu mazabu suka hana faruwar hakan, ta hanyar mayar da martani kan ‘yan bangar siyasar har sai da suka tabbatar sun fatattake su. 

Lamarin bai tsaya iya kan ‘yan bangar da ake ganin watakila akwai yarinta ko kuma rashin ilimi a tattare da su ba, inda jami’an yan sanda suka sanar da kama shugaban kamfanin sufurin motoci na  Kano Line, wato Bashir Nasiru Aliko, bisa zargin jagorantar yan daba su tarwatsa masu zabe, sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ya ji a jikinsa, domin kuwa sai da jama’a suka lakada masa dukan kawo wuka. 

A jihar Katsina kuwa wasu bayanai sun ce ‘yan bindiga sun tare tawagar dan takarar gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Nura Khalil, amma dai babu rahoton rasa rai ko kuma jikkata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.