Isa ga babban shafi

Tashe-tashen hankula da sayen kuri'a sun rage kimar zaben gwamnoni - Rahoto

Cibiyar bunkasa dimokaradiya a nahiyar Afrika CDD mai hedikwata a Birtaniya, ta ce an samu karuwar matsalar sayen kuri’u ta hanyar amfani da kudade ko musayar haja yayin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da ya gudana a karshen makon, idan aka kwatanta da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabarairu.

Wasu 'yan Najeriya yayin murna kan sakamakon da jami'an zabe suka bayyana a rumfar da suka kada kuri'a a jihar Lagos.
Wasu 'yan Najeriya yayin murna kan sakamakon da jami'an zabe suka bayyana a rumfar da suka kada kuri'a a jihar Lagos. AP - Sunday Alamba
Talla

Sai dai cibiyar ta yaba da yadda zaben gwamnonin da na  ‘yan majalisunsu ya gudana cikin kwanciyar hankali a akasarin sassan Najeriya, ba kuma tare da yawaitar korafin rashin aiki ko ingancin na’urorin tantance masu zabe na BVAS ba.

Darakatar ta CDD Idayat Hassan ta ce sun gina rahotonsu ne daga bayanan jami’ansu na sa ido fiye dubu 1,200 da ke fadin Najeriya.

Cibiyar bunkasa dimokaradiyar ta kara da cewar wakilan jam’iyyu, da kuma ‘yan bangar siyasar da aka dauka haya, gami da karancin jami’an tsaro, sun taka rawa wajen janyo fuskantar tashe-tashen hankula a wasu sassan jihohin Lagos, Rivers, Kano, Yobe, Kogi da kuma Enugu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.