Isa ga babban shafi

Ana dakon sakamako a yayin da ake tattara kuri'un zaben Najeriya

‘Yan  takarar da suka fafata a zabukan gwamna da na ‘yan majalisu a kasar gami da magoya bayansu na dakon yadda sakamako zai kaya, a yayain da hukumar zaben kasar ta fara tattara sakamako.

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya a Yola. 23 ga Fabrairu, 2023
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya a Yola. 23 ga Fabrairu, 2023 AP - Sunday Alamba
Talla

Andai  gudanar da zabengwamnoni  ne a jihohi 28 daga 36 da keNajeriya, yayin da kuma aka  yi  zabenyanmajalisundokoki a dukkaninjihohin. 

Bayanai sun cetuni  hukumarzabemai zaman kanta ta  farawallafasakamakonzabukan da sukagudana a shafintanayanargizo, matakin da a kansajam’iyyunadawa da kumawasujami’ansaidosukacaccakihukumar, sabodagazawallafa  sakamakonzabenshugabankasa da nayanmajalisundokokinkasar da yagudana a karshenwatanFabarairu. 

 Kasar da ta fi  fice a nahiyar Afrika na zaben sama da ‘ya  majalisun dokokin jihohi  900 da gwamnoni 28, kuma jihohin da aka fi gwada kwanji sune wadanda gwamnoninsu ke neman zarcewa a wa’adi na biyu, musamman ma  jihar Lagos da ke kudu maso yammacin kasar.

A Najeriya, mukamin gwamna dai mukami ne mai matukar girma da kima, ganin cewa su ke sarrafa kasafin kudin jihohinsu yadda suke so, hasali ma akwai jihohin da kasafinsu ya fi na wasu kasashe a nahiyar Afrika.

A yayin da zaben ya gudana cikin lumana a sassa da daman a kasar, wasu masu sa ido sun caccaki ‘yan siyasa a kan sayen kuri’u, inda suka zarge su da amfani da talauci a matsayin makami na tursasa wa masu zabe yin sabanin abin da ke zukatansu.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.