Isa ga babban shafi

Sakamakon zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki ya fara bayyana

An gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 28 yayin da aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a dukkan jihohin Najeriya 36,sa'o'i kadan bayan da 'yan Najeriya suka fara kada kuri'a a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki a fadin kasar, sakamakon zaben da aka gudanar ya fara karatowa.

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, yayin kidayar kuri'u a garin Lagos.
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, yayin kidayar kuri'u a garin Lagos. REUTERS/Adelaja Temilade
Talla

A Najeriya miliyoyin masu kada kuri'a ne suka yi rajista da kuma kada kuri'a a rumfunan zabe sama da 170,000 a fadin Najeriya.

Jihohi 28 da ke kasar ne  aka gudanar da zaben gwamnonin, da suka hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Kwara, Lagos, Nasarawa, Ogun, Oyo, Yobe da Zamfara.

Sauran sun hada da Abia, Akwa Ibom, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Naija, Filato, Rivers, Sokoto, da Taraba.

Rahotanni daga wasu yankunan na kasar na tabbatar da cewa an fuskanci 'yan matsaloli a wasu yankunan kasar,irin su Lagas,Ijebu da Sokoto.

Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya
Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP

Caleb wanda yana daya daga cikin masu sa ido da dama da ke aiki tare da Cibiyar Yada Labarai da Ci Gaba (CJID) ya ce wani soja da aka bayyana sunansa da Olukoya ya tare shi a kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Ijebu ta Arewa.

 Ban san dalilin da ya sa ya zabi ya bata lokacinmu ba amma na yi farin ciki yanzu ina Ijebu ta Arewa domin ci gaba da aiki na

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.