Isa ga babban shafi

Sanata Bala Muhammad ya sake lashe zaben gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya samu nasarar yin tazarce a zaben da ya gudana a ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad yayiin murnar sake lashe zabe da yayi.
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad yayiin murnar sake lashe zabe da yayi. © RFI Hausa/Ibrahim Malam Goje
Talla

Yayin sanar da sakamakon a yau Litinin, hukumar zabe ta ce Sanata Bala Muhammad ya samu kuri'u dubu 525,280, yayin da abokin hamayyarsa na APC tsohon shugaban hasfan sojin saman Najeriya mai ritaya Air Marshal Sadik Baba Abubakar ya samu kuri'u 432,272.

Dan takarar jam’iyyar NNPP Sanata Halliru Jika ne ya zo na uku a zaben gwamnan na Bauchi, da kuri’u dubu 60 da 496.

Sai dai wakilan wasu daga cikin jam’iyyun adawa sun yi watsi da sakamakon da aka bayyana, musamman na jam’iyyar APC wanda yaki sanya hannu bisa zargin cewa tashe-tashen hankula sun hana gudanar da zabe a rumfuna da dama, yayin da a wasu sassan kuma aka yi aringizon kuri’u fiye da adadin mutanen da aka  yi wa  rijista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.