Isa ga babban shafi

Peter Obi ya maka zababben shugaban Najeriya a kotu

Dan takarar zaben shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar Labour Peter Obi ya maka zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu, inda yake kalubalantar sakamakon zaben. 

Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour.
Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour. AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Obi da ya zo na 3 a cikin ‘yan takarar zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabarairu ya gabatar da bukatu guda 5 cikin su har da da bukatar soke zaben da kuma gudanar da wani sabo. 

Takardar karar wadda ke dauke da sanya hannu ‘dan takarar da kuma na jam’iyyarsa, ta sanya hukumar zabe ta INEC da zababben shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da Jam’iyyar APC a matsayin wanda take kara. 

Yau ranar 21 ga watan Maris ke zama cikon makwanni uku da doka ta bayar daga ranar 1 ga watan Maris da aka sanar da sakamako, domin duk wani mai korafi ya ruga kotu domin neman hakkinsa. 

Hukumar zabe ta bayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da kuri’u sama da miliyan 8 da dubu dari 800, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u sama da miliyan 6 da dubu 900, sai kuma Peter Obi na Labour da ya zo na 3 da kuri’u miliyan 6 da dubu 490. 

Lauyan Obi Livy Ozoukwu yace a lokacin da aka gudanar da zaben, Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba, kuma bai samu halartattun kuri’un da zasu bashi nasara ba. 

Ozoukwu ne ya jagoranci tawagar lauyoyin Atiku Abubakar domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2019 amma kuma basu samu nasara ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.