Isa ga babban shafi

Zaben gwamnoni: An bayyana sakamakon jihohi 24 daga cikin 28

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da sakamakon zabukan gwamna na jihohi 24 daga cikin 28 din da aka kada kuri’u kan kujerunsu a ranar Asabar din da  ta  gabata, 18 ga watan Maris.

Jami'an zabe yayin kirga kuri'u a Najeriya.
Jami'an zabe yayin kirga kuri'u a Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Tuni dai ta tabbata cewar wasu gwamnonin ko ‘yan takararsu sun sha  kaye a zaben na karshen mako.

Ya zuwa daren jiya Litinin dai, daga sakamakon da hukumar zabe ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe kujerun gwamnan jihohi 15, da suka hada da Yobe, Neja, Cross Rivers, Ogun, Ebonyi, Benue, Kaduna da Borno. Sauran kuma sun hada Lagos, Nasarawa, Sokoto, Katsina, Jigawa, Gombe da kuma Kwara.

Ita kuwa jam’iyyar PDP jihohi 8 ta dafe, da suka hada da Zamfara, Bauchi, Oyo, Filato, Taraba, Delta, Rivers da kuma Akwa Ibom. Yayin da jam’iyyar NNPP ta lashe zaben Kano.

Ragowar jihohin da ake dakon sakamakon su dai sun hada ne da wadanda hukumar INEC ta ce zaben kujerar gwamnan nasu bai kammalu ba, wato Kebbi da  Adamawa inda soke kuri’u akalla dubu 37 da 16 da aka kada a rumfunan zabe 69. Zuwa kuma lokacin da INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP ke kan gaba da kuri’u dubu 421, 524, yayin da Sanata Aishatu Binani ke da kuri’u dubu 390 da 275.

A Enugu da Abia kuma dakatar da aikin tattara sakamakonsu aka yi daga wasu kananan hukumomi saboda takaddamar da ta kaure tsakanin wakilan jam’iyyu musamman na Labour da PDP wadanda suka sam basu yarda da wasu alkaluman kuri’un da aka gabatar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.