Isa ga babban shafi

Jam'iyyar Labour ta lashe zaben gwamnan jihar Abia

An bayyana dan takarar gwamnan jam’iyyar Labour, Alex Otti a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Abia.

Magoya bayan jam'iyyar Labour kenan da ke nuna farin cikin lashe wata mazaba a zaben Najeriya.
Magoya bayan jam'iyyar Labour kenan da ke nuna farin cikin lashe wata mazaba a zaben Najeriya. AP - Ben Curtis
Talla

Farfesa Nnenna Oti, babbar jami’ar zaben jihar ce, ta bayyana Otti a matsayin wanda ya lashe zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben da yammacin Laraba.

Nnenna ta ce Otti ya samu yawan kuri’u 175,467 da aka kada massa, inda ya ssha gabana abokin karawar sa, Chief Okey Ahiwe na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wanda ya samu kuri’u 88,529 da aka kada masa.

Wannan ne karon farko da jam’iyyar Labour ta samu nasara a zzaben gwamnonin kasar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, a jihohin kasar 28.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.