An samu rarrabuwar kawuna tsakanin kabilun Yarabawa da Igbo a Legas
An samu rarrabuwar kawuna mafi muni tsakanin Kabilun Igbo da Yarbawa a jihar Lagos da ke kudancin Najeriya sakamakon yadda kowanne bangare ya fito karara ya nuna kabilanci a yayin zabukan da aka gudanar a jihar.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:06
Rahotanni na cewa, yanzu, da dama daga cikin ‘yan kabilar Igbo na rayuwa ne cikin dari-dari a Lagos musamman saboda barazanar hare-hare da suka fuskanta daga Yarbawa.
Wannan na zuwa ne bayan rashin nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu daga jihar a zaben shugabancin kasar da aka yi a cikin watan Fabrairu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Abdulrahman Gambo Ahmad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu