INEC ta yi taron kintsawa zaben gwamnoni a Najeriya
Hukumar zabe a tarayyar Najeriya tayi zama da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin kintsawa zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da za’a gudanar a ranar asabar 18 da watannan.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:06
Wannan na zuwa ne, bayan kwanaki da INEC din ta kara wa'adin mako guda na zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohin kasar, sakamakon abin da ta kira na sake fasalta na'urorin tantance masu kada kuri'a wato BVAS.
A ranar 25 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Najeriya, inda Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe zaben.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton da Muhammad sani Abubakar ya hada, daga Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu