Isa ga babban shafi

PDP ta maye gurbin Iyioricha Ayu bayan dakatar da shi

Kwamitin ayyuka nababbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya maye gurbin shugaban jam’iyyar Sanata Iyioricha Ayu.

Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP.
Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP. © dailytrust
Talla

A wani taron gaggawa da jam’iyyar ta yi a ranar Talata, kwamitin ya amince da umarnin babbar kotun jihar Benue, wadda ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce bayan yin nazari da kyau da umarnin kotu da kuma bin sashe na 45 (2) na kundin tsarin mulkin PDP da aka yi wa gyara a 2017, kwamitin ya yanke shawarar cewa Mataimakin Shugaban shiyyar Arewa, Ambasada Umar Ilyya Damagum shine zai rike shugabancin jam’iyyar.

Rikicin jam’iyyar bayan zaben kasar, ya dauki wani sabon salo a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da masu ruwa da tsaki na gundumar Igyorov a karamar hukumar Gboko ta jihar Binuwai suka dakatar da Ayu bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

An dauki matakin ne kwanaki kadan bayan kwamitin jam'iyyar ya kai gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom gaban kwamitin ladabtarwa tare da dakatar da wani tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da tsohon shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim da dai sauransu.

Dakatar da Ayu ya biyo bayan kuri'ar rashin amincewa da shi da shugabannin gundumar suka yi masa a karshen taron nasu.

Sakatariyar gundumar, Vangeryina Dooyum, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun 12 daga cikin mambobi 17 na gundumar, ta ce an cimma matsayar dakatar da shugaban na kasa ne bayan da shugabannin suka yi nazari a kan rawar da ya taka a karshen babban zaben 2023.

Ayu ya bayyana matakin a matsayin zancen wofi, inda ya ce duk wani tsagi na jam’iyya ko kwamitin zartarwa na jam’iyyar a matakin gunduma ko Jiha ba za ta iya daukar wani mataki na ladabtarwa ga duk wani dan kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa ba.

Amma daga baya wata babbar kotun jihar Benue ta hana shi bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDPn na kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.