Isa ga babban shafi

Kotu a Jigawa ta yanke hukunci kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane 3

Kotu a jihar Jigawa ta arewacin Najeriya ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu mutane 3 da aka samu da aikata muggan laifuka ciki har da kisan kai, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ta hanyar amfani da manyan bindigogi.

Ana dai tuhumar mutanen 3 da manyan laifuka ciki har da fashi da makami da garkuwa da mutane.
Ana dai tuhumar mutanen 3 da manyan laifuka ciki har da fashi da makami da garkuwa da mutane. © Humanists International
Talla

Yayin zaman kotun na asabar din nan karkashin jagorancin mai shari’a M.M Kaugama da kwamishinan shari’a na jihar Jigawa Dr Musa Adamu Aliyu, alkalin ya karanta hukuncin kisan ta hanyar rataya kan mutanen 3 wanda tuni gwamnatin jihar ta amince.

Akalla shaidu 5 suka tabbatar da aikata laifukan mutanen 3 yayinda kotun ta wanke mutum na 4 Ya’u mai Hatsi wanda aka gaza samunsa da laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Kotun wadda ta yi zama a karamar hukumar Kaugama ta samu Suleiman Bello da Auwalu Muhammad da kuma Yakubu Muhammad da tarin laifukan, ciki har da garkuwa da wata mata Hadiza Abdullahi da ke garin Marma a karamar hukumar Kirikasamma tare da neman biyan fansar naira miliyan 150.

Haka zalika yayin zaman shari’ar mutanen 3 sun kuma amsa laifinsu na kisan wani magidanci Audu Saje a karamar hukumar ta Kaugama.

Yayin sumamen da jami’an tsaro suka kai gidan mutanen 3 sun sanar da samun bindigogi kirar AK-47 guda 3 da wata babbar bindiga kirar GPMG sai carbin harsasai guda 9 kana harsasai na daban 309 sai kuma tsabar kudi Naira miliyan 2 da dubu 70 baya ga mashin wanda aka yi ittifakin na mutumin da suka kashe ne Audu Saje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.