Isa ga babban shafi

Najeriya ta bukaci Obi yayi bayani kan kalamansa da suka janyo cece-kuce

Gwamnatin Najeriya ta kalubalanci Peter Obi dan takarar shugabancin kasar a zaben da ya gabata a karkashin jam’iyyar Labour, da ya fito ya fayyace matsayinsa dangane da sakon sautin da aka yada na tattaunawar da ta gudana tsakaninsa da shugaban babbar Mujami’ar 'Living Faith' Bishop David Oyedepo.

Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban Najeriya na jam'iyyar Labour.
Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban Najeriya na jam'iyyar Labour. AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ne ya kalubalanci Obi, yayin wata ganawa da yayi da manema labarai ranar Litinin da ta gabata a birnin London.

A cewar Ministan, ya kamata dan takarar na Labour ya yi wa jama’a bayani kan abinda yake nufi da cewar, sautin da aka nadi muryarsa da ta Bishop na karya ne, wanda kuma aka yi amfani da wasu dabaru wajen samar da shi.

A farkon watan Afrilun nan, aka wayi gari da yaduwar sakon sautin da ke dauke da tattaunawar Peter Obi da Bishop Oyedepo, wanda cikinsa aka jiyo muryar dan takarar shugabancin Najeriyar na neman taimakon Bishop din da ya  ja hankalin mabiya addinin Kirista su goyi bayan takarar da yake yi, inda ya kuma bayyana zaben da ake tunkara a matsayin yaki na addini.

Sai dai daga baya Obi ya fito yayi watsi da sautin muryoyin, tare da bayyana shi a matsayin karyar da aka shirya domin bata masa suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.