Isa ga babban shafi

Adamawa: Matan Najeriya sun sake samun koma baya a siyasa

Yunkurin matan Najeriya na ganin sun samu mace ta farko da zata zama gwamnan jiha ya sake samun koman baya sakamakon rashin nasarar da Sanata Aisha Binani ta samu a zaben gwamnan jihar Adamawa da aka kammala a karshen mako. 

Aishatu Binani
Aishatu Binani © dailytrust
Talla

Bayan ‘dan tangardar da aka samu, Hukumar zaben Najeriya a yau ta sanar da gwamnan jihar Adamawa kuma dan takarar jam’iyyar PDP Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 430,861, yayin da Binani ta APC ta samu kuri’u 398,788. 

Gabatar da wannan sakamakon ya kawo karshen tirka-tirkar da aka samu a Jihar, bayan da shugaban hukumar zaben jihar yayi gaban kansa wajen sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta samu nasara ba tare da bin ka’idar hukuma ba. 

Wannan shine karo na biyu da mace ke zuwa daf da samun nasarar zaben gwamna a tarihin Najeriya kafin daga bisani kujerar ta kubuce mata. 

A shekarar 2019 Sanata Aisha Jummai Alhassan ta nemi kujerar gwamnan jihar Taraba har zuwa lokacin da ake ganin kamar ita zata ciri tuta wajen zama mace ta farko da zata zama gwamna, amma hakan bai yiwu ba ganin yadda hukumar zabe ta bayyana gwamna Darius Ishaku a matsayin wanda ya samu nasara. 

Ga alama zai sake daukar lokaci kafin samun macen da zata kawo karshen babakeren da maza suka yiwa kujerun gwamna da kuma shugaban kasa a Najeriya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.