Isa ga babban shafi

Ahmadu Fintiri ya sake lashe zaben gwamnan jihar Adamawa

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya sake lashe zaben gwamnan jihar, bayan fafatawa da ya yi da Aishatu Dahiru Binani, ta jam'iyyar APC, inda ya sha da kyar a hannunta.

Zababben gwamnan jihar Adamawa tare da abokiyar hamayyar sa Aishatu Binani
Zababben gwamnan jihar Adamawa tare da abokiyar hamayyar sa Aishatu Binani © dailytrust
Talla

INEC ta sanar da cewa, Aisha Binani daga jam'iyyar APC, ta samu adadin kuri'u 398,788, inda Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP ya samu yawan kuri'u 430,861.

Wannan dai na zuwa ne, bayan da babbar kotun tarayya da ke Abujan Najeriyar, ta ki amincewa da bukatar da Sanata Binanin ta gabatar mata, na neman ta dakatar da INEC, sanar da sakamakon wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Lokacin da lamarin ya zo a ranar Talata, Mai shari’a Inyang Ekwo ya umurci lauyoyin Binani karkashin jagorancin Mohammed Sheriff Esq da su yi magana a kan batun shari’ar a cikin kwanaki uku.

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton da wakilin RFI ya hada daga Yola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.