Isa ga babban shafi

Kotu ta fara sauraron kararrakin da ke kalubalantar nasarar Tinubu

Yau litinin kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta fara sauraron karar da ke kalubalantar nasarar shugaba mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu.
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu. AP - Ben Curtis
Talla

Bayan matakin jam’iyyar AA na janyewa daga kalubalantar nasarar Tinubu a zaben na watan Fabarairu yau litinin, yanzu haka jam’iyyu 4 ke kalubalantar nasarar zababben shugaban, da suka kunshi babar jam’iyyar adawa ta PDP, da LP da APP da kuma APM.

Tawagar lauyoyi daga bangarori daban-daban ne suka halarci taron kaddamar da fara sauraron korafe-korafen zaben na bana, wanda zai kunshi babban zaben shugaban kasa da kuma gwamnoni baya ga ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.

Yayin zaman kotun na yau a Abuja da alkalai 5 ke jagoranci dukkaninsu karkashin mai shari’a Haruna Tsammani, kotun ta sha alwashin gudanar da shari’ar bisa adalci ba tare da tauye hakkin kowanne bangare ba.

A jawabinsa gabanin fara sauraron bahasin kararrakin, Mr Tsammani ya gargadi lauyoyin da ke kare kowanne bangare da su kiyaye da amfani da salon da zai tsawaita lokacin shari’a yayin sauraron kararrakin.

A cewarsa wajibi ne a mutunta lokaci yayin zaman shari’un lura da cewa batutuwan zabe lamurra ne da ke tafiya da lokaci.

Tawagar alkalan da za su jagoranci zaman shari’ar dai sun kunshi Haruna Tsammani da Stephen Adah da kuma Boloukuoromo Moses Ugo sai Abba Mohammed da kuma Misitura Bolaji-Yusuf.

Lauyan da ke kare zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, Wole Olanipekun ya shaidawa zaman kotun cewa a shirye su ke su baiwa alkalai hadin kai don gaggauta gudanar da shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.