Isa ga babban shafi

Wata kungiya na neman kotu ta dakatar da rantsar da zababben shugaban Najeriya

Wasu mazauna babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja sun bukaci wata babbar kotu a birnin ta dakatar da rantsar da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu, zababben shugaban Najeriya.
Bola Tinubu, zababben shugaban Najeriya. AP - Ben Curtis
Talla

Mutanen da suka samu wakilcin lauyoyi kamar su, Anyaegbunam Ubaka Okoye, David Aondover Adzer, Jeffrey Oheobeh Ucheh, Osang Paul da Chibuke Nwachukwu, suna neman kotun ta dakatar da alkalin alkalan kasar, ko ma wani, daga rantsar da duk wani wanda ya yi takara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin shugaban kasa ko mataimaki.

Sun ce bukatar hakan ta zama   wajibi har sai an warware korafe-korafen zabe da ke gaban kotu, daidai da tanadin sashi na 134, karanmin sashi na 2.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da   Peter Obi na Labour wadanda suka zo na 2 da na 3 suna kalubalantar  sakamakon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.