Isa ga babban shafi

Na kadu da tattaunawar Blinken da Tinubu - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da akayi a watan Fabarairu Atiku Abubakar ya bayyana matukar kaduwarsa da tattaunaar da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yayi da zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 

Tinubu-Blinken
Tinubu-Blinken © leadership
Talla

Wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na facebook, Atiku ya bayyana tattaunawar a matsayin wadda tayi hannun riga da matsayin Amurka wadda tayi suna wajen kare muradun dimokiradiya bayan gamsassun bayanan da aka yiwa kasar akan irin magudin da aka tafka a zaben ranar 25 ga watan Fabarairu. 

Atiku yace halarta zaben Najeriya da Amurka tayi wajen tattaunawar Blinken da Tinubu zai sanya gwuiwar jama’ar kasar wadanda suka dogara da dimokiradiya yayi sanyi. 

Wannan matsayi na zuwa ne kwana guda bayan tattaunawar da Tinubu yayi da Sakataren inda suka jaddada aniyar aiki tare tsakanin Amurka da Najeriya da zarar an rantsar da zababben shugaban kasar a ranar 29 ga watan Mayu. 

Sanarwar da mai magana da yawun Tinubu Tunde Rahman ya sanyawa hannu tace, Blinken ya taya zababben shugaban murnar nasarar da ya samu, yayin da ya janyo hankalinsa akan ci gaba da kare muradun dimokiradiya da kuma gina kasa wajen hada kan al’ummar ta tare da shawo kan matsalolin da suka addabe ta, yayin da ya sha alwashin ganin Amurka da Najeriya sun yi aiki tare. 

A nashi jawabi, Tinubu ya jinjinawa Amurka wadda ta bashi mafaka lokacin da Janar Sani Abacha ya tilasta masa tserewa daga Najeriyar, inda ya shaidawa Blinken aniyarsa ta dinke barakar da aka samu na rarrabuwar kawunan jama’ar kasa da kuma shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arzikin Najeriya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.