Isa ga babban shafi

Abba ya yi mamakin rashin bayyanar Ganduje a wajen bikin rantsuwa

A jawabinsa gaban taron rantsar da shi yau litinin, sabon gwamnan Kano Injiniya Abba kabir Yusuf ya diga ayar tambaya game da dalilin da ya hana tsohon gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje halartar wajen bikin mika mulkin ga sabuwar Gwamnati.

Sabon Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Sabon Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf. © Infotrust
Talla

Sabon Gwamnan na Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf lokacin da ya ke jawabi a filin wasa na Sani Abacha a Kano, inda ake ci gaba da bikin rantsuwar kama aikin sabuwar gwamnatin, ya yi shaguben cewa ko tsohon gwamnan na Kano na tsoron halartar wajen ne.

Wasu daga cikin hotunan bikin rantsar da sabon Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Wasu daga cikin hotunan bikin rantsar da sabon Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. © RFI-Dandago

A cewar Abba Kabir ya gaji bashin fiye da Naira biliyan 200 daga gwamnatin Ganduje, inda ya ce gwamnatin sa za  ta bi diddigin yadda aka kashe wadannan kudade.

Wani bangare na taron bikin rantsar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Wani bangare na taron bikin rantsar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. © RFI-Dandago

Tsohon sakataren gwamnatin Kano Usman Alhaji ne ya mika mulkin a madadin tsohuwar gwamnatin ta Ganduje.

 

Hotunan bikin rantsar da Abba Kabir Yusuf.
Hotunan bikin rantsar da Abba Kabir Yusuf. © RFI-Dandago

Zuwa yanzu dai ana ci gaba da shagulgulan murnar mika mulkin ga Abba Kabir Yusuf wanda ya yi nasarar lashe zaben watan Fabarairu da gagarumin rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.