Isa ga babban shafi

Babu mahalukin da zai rusa sabbin masarautun Kano - Ganduje

Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya Abdullahi Umar Ganduje yace babu wani mahaluki da zai taba sabbin masarautun jihar guda 4 da ya kirkiro domin haifar da ci gaba a kowanne sashe na jihar. 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarkin Bichi Mai Martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarkin Bichi Mai Martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero. © Solacebase
Talla

Ganduje ya shaidawa taron ma’aikatan jihar da suka halarci bikin ranar ma’aikata ta duniya cewar Allah ba zai baiwa wani mahaluki damar ruguza su ba, kamar yadda wasu ke hasashe yanzu haka. 

Gwamnan mai barin gado ya bayyana masarautun a matsayin wani ginshiki na hadin kai, ci gaba da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar. 

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayin gabatar da Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayin gabatar da Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero © Daily Trust

Ganduje yace a wannan lokaci duk wanda ya ziyarci sabbin masarautun zai ga irin ci gaban da aka samu, wadanda suka dada daga darajar al’adun jama’ar dake yankunan da kuma girmama su. 

Gwamnan ya bayyana cewar koda basa cikin gwamnati, zasu ci gaba da yin addu’oi ga Ubangiji domin kare wadannan masarautu. 

Wadannan kalamai na gwamnan mai shirin barin gado na zama tamkar wani martani ne ga kalaman tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yake cewa sabuwar gwamnati da zata karbi mulki a karshen wannan watan zata duba makomar sabbin masarautun da kuma tube tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2 da gwamna Ganduje yayi. 

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje © This Day

Tuni aka samu rarrabuwar kawuna a Jihar dangane da wadannan kalamai tsakanin masu goyan bayan sabbin masarautun da kuma wadanda ke ganin cewar ba’a yiwa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi adalci wajen tube shi da kuma karkasa masarautar Kanon ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.