Isa ga babban shafi

Kada a saki Nnamdi Kanu - Asari Dokubo ga Tinubu

Tsohon jagoran tsagerun Niger-Delta a Najeriya, Asari Dokubo, ya ce sakin Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kasar Biafra (IPOB), zai kasance tamkar bude kofa ne ga masu aikata manyan laifuka.

Kanu-Asari-Dokubo
Kanu-Asari-Dokubo © premiumtimes
Talla

Kanu wanda ke fuskantar shari’a kan ayyukan ta’addanci, yana tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS tun bayan sake kama shi a shekarar 2021.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa a shekarar 2017 amma ya bijirewa sharuddan belin daga bisani ya tsere daga kasar.

Tsohon shugaban kasr Muhammadu Buhari ya bijirewa matsin lamba na a saki Kanu, amma da shigar sabuwar gwamnati, an sake yin kiraye-kirayen a saki shugaban na IPOB.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasar Bola Tinubu, Dokubo ya ce kamata ya yi Nnamdi Kanu ya fuskanci doka.

Dokubo ya ce a halin yanzu Najeriya na fama da yakin basasa a sassa daban-daban na kasar, inda ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara matakan tsaro domin ‘yan kasa su samu damar tafiye-tafiye da kuma harkokin kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.