Isa ga babban shafi

Gwamnoni na amfana da rikicin IPOB a kudancin Najeriya - Dan majalisa

Wani ‘dan majalisar wakilai daga Jihar Imo a Najeriya, Ikeanga Ugochinyere ya bayyana cewar wasu daga cikin gwamnonin dake yankin kudu maso gabas na amfana da tashe tashen hankulan da ake samu a yankin, shi yasa suka kasa daukar matakan da suka dace domin shawo kan kashe kashen da ke faruwa. 

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra. http://naijagists.com
Talla

Ugochinyere yace Najeriya na da karfin da zata iya amfani da shi ta fuskar tsaro domin murkushe wadannan matsalolin da suka addabi yankin, amma dole sai shugabannin da suka fito daga kudu maso gabas sun zauna domin daukar matsayin bai-daya wanda za’ayi amfani da shi domin magance matsalar. 

‘Dan majalisar yace abinda suke bukata shi ne samun dauwamammen zaman lafiya a kudu maso gabas, saboda yadda yankin ya tabarbare, ganin kashe kashen da ake samu da lalacewar muhalli da rushewar kayan more rayuwa, amma wadanda ba zasu samu ba muddin babu zaman lafiya. 

Ugochinyere yace duk wani shugaban dake bukatar ci gaba da kuma hadin kan Najeriya, dole ya bude kofar sa domin baiwa masu ruwa da tsaki damar gabatar da shawarwari akan yadda za’a kawo karshen wannan matsala. 

‘Dan majalisar ya bayyana aniyar sa ta ganin sabuwar gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu a matsayin wata kofar da zata bada damar samun ci gaba da kuma hada kan jama’ar kasar. 

Yanzu dai kusan shekaru biyu Kenan da kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu ta kaddamar da shirin tilastawa jama’ar yankin zama a cikin gidajen su kowacce litini domin tilastawa gwamnati sakin shugaban na su wanda ke fuskantar zargin cin amanar kasa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.