Nnamdi Kanu ya umurci mukarabansa su kawo karshen rikici
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, ya umarci daya daga cikin mukarabansa Simon Ekpa da ya kawo karshen tayar da kayar baya a yankin kudu maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Ekpa na daya daga cikin kwamandojin Kanu kuma shi ne ya yi ikirarin cewa ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ta IPOB bayan tsare Kanun.
Jagoran kungiyar ta IPOB da ke tsare yanzu haka, a cikin wasikar da ya rubuta da hannu zuwa ga Simon Ekpa, ya bukace shi da ya yi sanarwar amincewa da karbar umarni daga gare shi.
Aloy Ejimakor, lauya na musamman dake kare Nnamdi Kanu, ya wallafa labarin wasikar da shugaban kungiyar ta IPOB ya rubuta da hannu a shafin sa na Twitter da aka tabbatar a jiya Juma’a. lauyan, a wata sanarwa da ya fitar dauke da wasikar, ya ce Nnamdi Kanu ya rubuta wasikar ne a ranar 24 ga watan yuli lokacin da daya daga cikin mukarabansa a yunkunri na kafa kasar Biafra, Simon Ekpa ya ziyarce shi a ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (SSS).
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu